kalaman yabon budurwa

kalaman yabon budurwa

kalaman yabon budurwa

 

Barka da zuwa ingantaccen shafin mu domin nishadi

Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba, masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya.

 

SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.

 

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

 

KE CE MURMUSHI NA.

 

Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

 

SINADARIN RAYUWA TA.

 

SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

 

ZAN SO KI JI.

 

Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!

 

auniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?

 

kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke

Har a yanzu zamu…

Ke dai taho gare ni dauke da kauna za ki gane ni ne na ki..ba ni da ta cewa sai godia ga Allah da ya ba ni yar fara mai fararen idanuwan da suka dace da kyakkyawan hancinta wanda ya yi daidai da kyakkywan kumatunki…wanda ya sa kika zarce sauran mata a kyau.

Yi murmushi idan kaga mai sonka, zai ji dadi. yi murmushi idan kaga mai kinka, zaiji tsoro. yi murmushi idan kaga wanda yabarka, zai yi dana sani. yi murmushi idan kaga wanda ka sani da wanda baka sani ba. murmushi kwarjinine ga namiji, adone ga fuskar mace. ku kasance masu yawan yin murmushi saboda nuna farinciki a rayuwa. banda yawan dariya domin tana kashe zuciya. Allah Kasa Mu Dace Ameen.

Masoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?

 

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.

Idan har na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na san irin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka. Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa, wannan sakon duciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.

A FARKON HA’DUWAR KU DA ITA

A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?

Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.

Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kud’inka. A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.

A dukkan lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.

Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da wad’annan abubuwa kamar haka;

Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.