Kalaman so ga budurwa
Assalamu Alaikum Warahamatullah! Yan’uwa Barka Da Wannan Lokaci Mai Albarka
Da Farko Zance Duk Lamarinda Zaka Gina To Ka Ginashi Akan
Turba Ta Gaskiya. Domin Ita Soyayya Gaskiya Ce, Amma
Marasa Gaskiya Kan Shigeta Har Su Batata Koma Su Tozartata
Nayi Nazari Akan Wasu Kalamai Na Soyayya Amma Ga Wanda
Yassan Zaiyi Soyayya Ta Nufin Yin Aure Ba Karyar Kurege Ba,
Wallahi Insha Allah Indai Da Nufin Aure Kake Ta Wadannan
Kalama Zasu Tai Maka Maka Kwarai Matuka, Kada Ka Bata
Lokacinka Ga Soyayya Da Babu Nufin Aure Acikin Ta Koda Kayi
Bazakayi Nasara Ba, Kuma Kaima Sai Anyi Da Diyarka!!! Anya
Zaka So Ayima Diyarka Karyar Soyayya?? Hmmm Nasan
Mai Karatu Bazai So Haka Ba, To Kada Kayi Dan Allah. To Bari
Mushiga Kai Tsaye Cikin Karatun Mu.
Kasan Amfanin Auren Mata Da Yawa? Yana Da Kyau
Shiga Karanta
Idan Kana Tare Da Budurwa / Masoyiyarka, Yana Da Kyau Ka
Kasance Kanayi Mata Kalamai Masu Dadi Na Jan Hankali,
Wadanda Zasu Dinga Faranta Mata Rai, Saboda Su Mata Haka
Suke So, Matukar Baka Yin Kalaman Soyayya To Anbarka
Abaya.
Daga Cikin Kalaman Da Muka Tsara Gasu Kamar Haka
Na Dade Ina Kallon Taurarin Samaniya Yayinda Naga Wacce Tafi
Kowacce Haske, Saina Naga Bakowa Bace Nike Ganiba Sai Ke
Masoyiyata!
So Gamon Jinine, Haqiqa Sonki Ya Zamo Jinin Jikina Ta Yadda Ya
Mamaye Zuciya Ta Bana Tunanin Kowa Sai Ke!
Soyyya Zalla: Zafafan Kalaman Soyayya Zalla Ga Masoya
Kinfita Daban A Cikin Mata, Duk Lokacin Da Na Kallleki, Sai Naga
Kamar Babu Kyakykyawar Mace Sai Ke!
Ki Kwantar Da Hankalinki Masoyiyata Babu Wata A Zuciyata Sai
Ke Kadai!
Kalaman so ga budurwa
Yarda Da Amincewar Ki Gareni, Sune Zasu Tabbatar Da Soyayyar
Ki Ta Gaskiya A Gareni!
Farin Ciki Baya Dorewa A Rayuwa Sai Tare Da Bakin Ciki, Dan
Haka Kowane Hali Nike Bazan Ta6a Mantawa Dake Ba
Masoyiyata!
Nakan Raba Dare Ina Mai Roqon Allah (S.W) Don Neman Biyan
Buqata, Ko Kinsan Kece Abu Na Farko Da Nike Roqon Samu!
Soyayya: Manya Manyan Kayataccin Kalaman Sace Zuciya
Domin Masoya Masu Soyayya.
Yanayin Sanyi Kan Sa Mutum Ya Takura, Tare Da Lulluba Da
Qaton Mayafi Amma Ni Duk Sanyin Da Ake Idan Na Tunaki Sai
Naji Tamkar Yanayin Zafi!
Yana da matukar kyau kadan rera ma budurwar ka baituka masu nuna soyayya cikin kalamai masu sace zuciya
Kin san so ba a mai kulle,
Gararinsa yawa na ‘yan talle,
Shuhurarsa a zuciya zille,
A ganta a fuska ba kyalle,
A san ya zarce duk komai.
Idan na taho a motata,
Cikin tafiya ta ƙasaita,
Idan na gane ki ‘yar auta,
Kina tafiya ta ƙasaita,
Na manta batu na tukin dai.
Kalarki daban a mataye,
Sunanki daban na ‘yar yaye,
Sautinki daban a Karaye,
A soyayya ana maye,
A sonki ko za na yo komai.
Naman da ake kira soye,
A cakuɗa kafi zabaye,
A sa naman a sa maye,
A sa gishiri a yo soye,
A so haka duk ake komai
Zaka iya ci gaba da kalaman so ga budurwar ka ko wane irin lokaci
Kamar Yadda Kowacce Bishiya Kanyi Rassa A Sama, Kuma Tayi
Saiwa A Qasa, Haka Sonki Ya Mamaye Dukkan Jikina,
Idan Na Kalleki Sai Nayi Farin Ciki, Idan Naji Tattausan Muryarki,
Sai Nishadi Da Walwala Tare Da Annashuwa Gami Da Farin Ciki Su
Mamaye Zuciyata! Abokina Ahakan Zaka Bi Don Sace Zuciyar
Masoyiyarka Cikin Sauki!
Siffar Ki Da Halayenki Sune Abin Yabawa Ga Duk Da Namiji
Musamman Ni, Kefita Daban Acikin Mata
Nayarda Da Ke Saboda Kyakykyawar Surar Jikinki, Ga Kamun Kai
Da Sanin Yakamata Matama Da Irinki Soke Yin Koyi Wallahi Ina
Sonki.
Domin Mata: Kina Soyayya? Ko Kinada Mai Sonki? Karanta
Wannan Sakon
Kalaman Zasu Iya Sauyawa Zuwa Lamiri/Jinsin Namiji, Saboda
Haka Kema Zaki Iya Juya Turn Na Wannan Kalaman Domin Sace
Zuciyar Masoyinki Cikin Sauki!! In Kuma Kinyi Musu Ku Jaraba
Kugani!!
Daga Karshe Ina Son Mai Karatu Yafahimci Cewa Kalaman
Soyayya Suna Tasiri Ne Kadai Idan Dama Akwai So Tsakanin
Saurayi Da Budurwa Ko Mata Da Miji, Idan Kasan Babu So Tun
Farko To Kada Ka Bata Lokacin Ka.
Allah Yasa Soyayya Ce Ta Nufin Ayi Aure. Madallah da karanta wannan sako na soyayya: kalaman so ga budurwa