Gwamna Babagana Umara zulum Ya Yabawa Daukacin Mutanen Jahar Barno

Gwamna Babagana umara zulum ya yabawa daukacin mutanen Jahar Barno da Suka karbi Bakuncin shugaba buhari

Gwamna  Zulum ya mika godiyar ga daukacin mutanen jahar Borno, bisa ga gagarumar fitowar da sukayi dubbai-dubbai mazan su da mata, tsofaffi da yara da sukayi a ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jahar ta borno.

Shugaba Buhari ya shiga Jahar ne ta Borno domin kaddamar da aikin raya kasa da Gwamna Zulum ya aiwatar a jahar domin cigaba da jin dadin mutanen jahar.

Zulum yayi wannan gagarumin yabon ne a lokacin da yake zantawa da wasu muhimman mutane masu ruwa da tsaki bayan ziyarar shugaba Buhari a ranar alhamis.

Borno maiduguri

Gwamna  Babagana Umara Zulum yace yana matukar godiya ga al’umma musamman mutanen mazauna maiduguri da jere da suka fito suka nuna soyayyar su ga shugaba buhari.

 

Jahar Borno da Gwamna  Zulum

Shekaru masu yawa jahar ta Borno ta kasance cikin halin hare-haren yan boko haram da suka tuso jahar da miyagun hare-hare, inda suke kisan rayuka da kone dukiya da lalata ma’aikatu da gidaje.

Halin da ya tusa ma mutanen jahar  matsanancin tsoro kenan har dayawa suka guje daga jahar, sannan ziyarar jahar yayi wahala daga yankuna daban daban.

Karanta wannan

An sake bude Kasuwar Shinkafi Zamfara state Maraba da samun zaman lafiya

Al’amarin ubangiji sauki gare shi idan ya tashi yima bayin sa mafita sai ya samar masu ita cikin sauki. Muatnen jahar Borno basu aune ba sai Allah ya kawo masu mafita wato gwamna umara zulum.

Borno city

Gwamna babagana Zulum mutun ne mai matukar adalci mai tsoron Allah, mai tausayin talakawan sa, mai son Al’umma. Da kyakkyawar niyyar sa ta son taimakon mutanen jahar Borno ya samu galaba akan yan boko haram da sauran yan ta’adda a cikin jihar da wajen ta da taimakon ubangiji. Yanzu jahar ta Borno ta koma abar kwaikwayo, abar so, daga sassa daban-daban na Najeriya. Barka da aiki jan gwarzo namijin duniya gwamna Babagana umara Zulum.

Share your love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *