An sake bude Kasuwar Shinkafi Zamfara state Maraba da samun zaman lafiya

An sake bude Kasuwar Shinkafi Zamfara state Maraba da samun zaman lafiya

Shinkafi zamfara state, da ke arewacin Zamfara state tana cikin karamar hukumar da ke cikin matsanancin tashin hankali sakamakon hara-haren yan bindiga da suke kaiwa ba kakkautawa.

Wanda sanadiyar wadannan hare-hare al’umma suka dauke ma hanyar shinkafi kafa ballantana kasuwar shinkafi.

Wakilan mu sun tattauna da wasu haifaffun karamar hukumar shinkafi da suka bar shinkafi din kwata-kwata tare da niyyar bazasu dawo mata ba har abada. Wannan hali ya hana zurga-zurgar motoci da kara tusa tsoro acikin zukatan direbobin hanyar.

Amma a yau alhamis 23/12/2021 wani abin mamaki da murna ya faru. Inda mutane daga yanki daban-daban suka ziyarci kasuwar cikin nutsuwa suka yi kasuwancin su harda murnar samun riba mai tsoka ba tare da wani jin tsoro ba.

Ku karanta wannan

Nafisa Abdullahi ta FIM din  Labarina ce tafi kowa ne Jarumi Shahara a Kannywood inji shafin Google

Musics

Auta MG Boy Inda aKwai Kauna to AKwai Yarda Hausa Song download

 

Misalin karfe 4:00pm na yamma mun samu damar ganaws da wandanda suka ci kasuwar ta shinkafi  har sun nuna farin cikin su sosai da nasara.

Shinkafi yanzu na Kara samun zaman lafiya wanda hakan na nuna karin nasara da jami’an tsaro ke samu.

Idan muka waiwaya baya shin ko mai karatu yasan tarihin shinkafi zamfara state? ko kun taba ziyarar garin? ko kuna da asali ko dangantaka da garin shinkafi?

Asalin jin tsoron bin hanyar shinkafi zamfara state.

kafin yanzu hanyar zuwa shinkafi tana daukar dubban baki daga yankuna daban-daban da suka hada da yan makarantar kimiya dake garin shinkafi, yan kasuwa da sauran su. Duk da cewa ko a wancan lokacin hanyar garin na fuskantar matsalar hare-haren yan ta’adda, amma sai da banbancin a wancan lokaci yan ta’addan suna karbar dukiya da wasu kayan da suke bukata, amma kam yanzu rayuwar mutane suke bukata suga bayanta.

Farashin zurga-zurgar mota daga kaura namoda zuwa shinkafi zamfara state a yanzu

Naira 250-300 ake zuwa garin shinkafi daga kaura namoda nisan da bai wuce kilomita sittin ba 60, amma yanzu naira dubu da dari biyar ne 1500, sannan kuma babu yakinin samun samun motar.

Direbobi da yan kasuwa a hanyar shinkafi zamfara State

Kashi tis’in na direbibin hanyar shinkafi sunyi murabus daga aikin su saboda shakku da tashin hankalin wannan hanya, haka suma yan kasuwar da yawa suka daina cin kasuwar.

A cikin garin shinkafi zamfara state

Garin shinkafi sai da yazamo mafi rashin jin dadin zama a zamfara, saboda tsoro da matsanancin fargaba yan ta’adda. Rayuwa tayi tsada, jin dadi ya nisanci garin sannan babu hanyar tserewa garin.

Nasarar jami’an tsaro a yankin na shinkafi

Yanzu rayuwa ta fara daukaka da jin dadi saboda samun saukin ta’addanci a hanyar da kuma garin na shinkafin, inda yan kasuwa har sun dan fara cin kasuwar bisa a baya da suka dauke mata kafa kaf

Share your love

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *